Bangaren kasa da kasa, dubban palastinawa sungudanar da zanga-zangar la’antar gwamnatin Amurka a garin Ramallah da ke gabar yamma da kogin Jordan, dangane da matsayin da gwamnatin ta Amurka ta dauka na kin amincewa da kafa kasar palastiny mai cin gishin kanta.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na nowlebanon cewa dubban palastinawa sungudanar da zanga-zangar la’antar gwamnatin Amurka a garin Ramallah da ke gabar yamma da kogin Jordan, dangane da matsayin da gwamnatin ta Amurka ta dauka na kin amincewa da kafa kasar palastiny mai cin gishin kanta a kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya.
A bangare guda kuma jami’in da ke kula da harkokin addini na yankin khalil Zaid Aljabbari ya sheda cewa, a ci gab ada tsokanar musulmi palastinawa yahudawan sahyuniya sun rufe masallacin annabi Ibrahim da ke garin Alkhalil tare da hana dubban palastinawa yin salloli a cikinsa ranar jiya baki daya.
Zaid ya ci gab ada cewa yahudawan wadanda dukkaninsu ‘yan share wuri zauna ne da suke zaune a wasu matsugunnai da suke kusa da yankin, sun shigo garin khalil dauke da makamai, inda suka rufe dukkanin kofofin masallacin, wadanda musulmi suke shiga domin isa zuwa ga babban ginin msallacin da suke yin ibada.
873874