IQNA

Akalla Mutane 8 Sun Mutu Wasu Sama Da 22 Sun Jikkata A Ta’iz

16:33 - October 06, 2011
Lambar Labari: 2199992
Bangaren kasa da jasa, a ci gaba da gudanar da zangar-zangar kyamar gwamnatin Yemen shugaba saleh na ci gaba da yin amfani da karfi domin murkushe masu bore a garuruwan da ke kudanicn kasar da kuma birnin San’a fadar mulki.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Aljazeera cewa, a ci gaba da gudanar da zangar-zangar kyamar gwamnatin Yemen shugaba saleh na ci gaba da yin amfani da karfi domin murkushe masu bore a garuruwan da ke kudanicn kasar da kuma birnin San’a fadar mulkin kasar ta Yemen.
Dubban daruruwan mutane suka gudanar da gangami a daren jiya tsakiya a birnin San'a, inda suka yi kira ga shugaba Ali Abdullah Saleh da ya gaggauta yin murabus daga shugabancin kasar.
Masu zanga-zangar sun yi ta rera taken da ke yin kira da a gurfanar da shugaba Abdallah Saleh tare da wasu daga cikin iyalansa a gaban kuliya domin hukunta su, kan kisan kiyashin da suke yi kan al'ummar Yemen, haka nan kuma masu zanga-zangar sun yi Allawadai da kasashen da suke mara wa shugaba Saleh baya, musamman ma Amurka da Saudiyya da suke ba shi dukkanin taimako domin murkushe fararen hula masu zanga-zangar lumana a kasarsa.
Mai aiko ma gidana talabijin na al'alam rahotanni daga kasar Yemen ya sheda cewa; jami'an tsaron kasar Yemn din sun bude wuta kan masu boren, inda suka kashe mutane biyu, suka kuma jikkata wasu da dama, hakan nan kuma sun kashe wasu fararen hula bakwai a lokacin da suka bude wuta kan wasu masu zanga-zanga a garin Ta'iz mai tazarar kilo mita 270 a kudancin birnin San'a.
873836



captcha