IQNA

Abin da ke Faruwa A Yankin Gabas Ta Tsakiya ya Mayar Da Isra’ila Saniyar Ware

17:05 - October 06, 2011
Lambar Labari: 2200002
Bangaren kasa da kasa, sra’ila na ci gaba da kara zama saniyar ware a tsakanin kasashen yankin dama wasu kasashen duniya, hakan ya kara fitowa fili ne bayan jawabin sakataran tsaron Amarika Leon Panetta da yayi tsokaci a yankin a yayin wata ziyara da ya kai yankin Palesdinu da aka mamaye.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a lokacin da yake batun halin da ake ciki a yankin gabas ta tsakiya, jagoran Pentagone ya bayyana cewa akidar sahayoniya na kara zama saniyar ware a yankin, ya ce kuma dole kasar Amarika ta sake tunani da nazari kan harakar tsaro dangance da Tel-Aviv. Yunkurin juyyin-juyya halin al'umma a yankin gabas ta tsakiya, da yadda tsananin tsanar HKI ke kara samun gurin zama a zukatan jama'a, da yadda ma ake tir da Allah wadai ga kasashen da suka yi yarjejeniyar zaman lafiya da HKI, sune dalilan da suka sa aka kara ware HKI a yankin.

Kasar Amarika da take tallafama HKI, tun 1948 na daukan ta kamar wani jigonta a fuskar siyasa da aikin soji a yankin, don zartas da siyasar washinton a gabas ta tsakiya. Duk jagororin kasar Amarika, a kullum, suna tsaye a kan wannan manufa ta siyasar kasarsu a ketare: Na farko cikakken goyan baya ga HKI, na biyu yadda za a fitar da ita daga wannan hali na kasancewarta saniyar ware a yankin gabsa ta tsakiya.
Tun daga 1991 kasar Amarika na ta faman ganin an samu sulhu na zaman lafiya a tsakankanin kasashen yankin amma ina abu sai kara lalacewa yake yi, don haka take so ta rage goyan bayan da take ba tsarin sahayoniyanci na sama da shekaru 40. Shekaru 20 bayan yarjejeniyar zaman lafiya ta Oslo, har yanzu ba a kai ga samun zaman lafiya a gabas ta tsakiya ba, don haka manyan jagororin kasar Amarika irinsu Leon Panetta su fito hili su bayyana kasawarsu ga duniya baki daya.
Babu yadda za a yi HKI ta rayu in ba da tallafin kudi daga kasar Amarika ba, bare kuma a yanzu da akidar Sahayoniyanci ke ci gaba da rasa magoya bayan ta a yankin irinsu Hosni Mubarak, na Masar ko Egypte.
Ko wace shekara Congres kin Amarika na amincewa da tallafin kudi million dubu 3 don samar da makamai da kayan sojoji ga HKI, sannan da hasassa tseren makamai a yankin. Kasar Amarika na so ta hana durkushewar kamfanoninta na kera makamai.
Shekaru 63 bayan kirkiro HKI Tsarin sahayoniyanci na ci gaba da kara samun makiya a duniya. Kan haka ne sakataran tsaron Kasar Amarika Leon Panetta da ke gaban wannan gagarumar guguwar boren jama'a a yankin gabas ta tsakiya, ya bayyana halin da HKI ke ciki a yau da babban bala'i.
873403

captcha