IQNA

Jam'iyar Al-wifaq Ta Yi Allawadai Da Kisan Wani Matashi A Kasar Bahrain

15:39 - October 08, 2011
Lambar Labari: 2200989
Bangaren kasa da kasa, jamiyar adawa ta Al-wifaq a kasar Bahrain ta yi kakkausar suka da yin Alawadai da mahukuntan kasar kan kisan da suka yi wa wani matashi da ya shiga cikin zanga-zangar neman sauyi a kasar.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Al-intiqad cewa, jamiyar adawa ta Al-wifaq a kasar Bahrain ta yi kakkausar suka da yin Alawadai da mahukuntan kasar kan kisan da suka yi wa wani matashi da ya shiga cikin zanga-zangar neman sauyi a kasar, inda kuma suka tarwatsa masu yi masa janaza a jiya.

Wani labarin kuma yana cewa, jaridar Daily Telgraf ta kasar Birtaniya ta habarta cewa gwamnatin Birtaniya ce ta horar da sojojin Saudiyya da suke murkushe fararen hula masu zanga-zangar lumana a kasar Bahrain.

Jaridar ta bayyana hakan ne a cikin bugunta na jiya Juma'a, bayan da karamin minista a ma'aikatar tsaron kasar ta Birtaniya Nick Harvey ya fito fili ya tabbatar da cewa; su ne suka horar da dakarun Saudiyya da suke gadin masarautar kasar, wadanda kuma su ne aka tura zuwa kasar Bahrain domin kare masarautar kasar daga boren al'umma, inda yanzu haka suke ci gaba da yin kisan gilla a kan fararen hula masu zanga-zangar lumana domin neman sauyi a cikin harkokin mulkin kasar.

Jaridar Telgraf ta ce tun kafin wannan lokacin an yi ta zargin cewa Birtaniya tana da hannu a murkushe zanga-zangar neman sauyi a kasashen Bahrain da Saudiyya, wanda hakan ke nuna irin siyar harshen damo da kasar ke bi kan batutuwa da suka shafi boren al'ummomin larabawa, inda take mara baya kai tsaye ga gwamnatocin Saudiyya da Bahrain, a bangare guda kuma tana adawa da gwamnatin Syria saboda wasu dalilai na siyasa.

874924

captcha