Bangaren kasa da kasa: Sheikh Hasan Alsifar jagoran yan shi'a a kasar Saudiya a cikin hudubar sallar juma'a da ya gabatar ya maida martini kan cin fuskar da mai huduba a Masallacin nabiyi tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa tsarkaka ya yi way an shi'a tare da jaddada cewa; malan wahabiya babu wani abu da suke nema sai tada fitina da rurata a tsakanin mabiya addinin musulunci.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai tsarki a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; Sheikh Hasan Alsifar jagoran yan shi'a a kasar Saudiya a cikin hudubar sallar juma'a da ya gabatar ya maida martini kan cin fuskar da mai huduba a Masallacin nabiyi tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa tsarkaka ya yi way an shi'a tare da jaddada cewa; malan wahabiya babu wani abu da suke nema sai tada fitina da rurata a tsakanin mabiya addinin musulunci. A ranar sha biyar ga watan Mehir na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya Sheikh Ali Alhuzaifi a lokacin yana gabatar da hudubar sallar juma'a ya yi dirar mikiya da yin kaca-kaca day an shi'a a wani mataki n ahaddasa fitina da rikici a tsakanin mazhabobin addinin musulunci lamarin day a fuskanci suka da maida martini daga manyan malama da shugabannin addini.
875485