IQNA

MDD Ta Amince Da Yi Wa Likitar Nan Yar Bahrain Sharia A Kotun Farar Hula

Bangaren kasa da kasa: majalisar dinkin duniya ta yi amanna da yi wa likitocin nan su ashirin shari'a a gaban kotun farar hula bat a soji ba bayan da ta soki matakin yi masu shari'a a gaban kotun soji a baya amma matsin lamba da suka ya sa mahukumtan da gwamnatin Bahrain canja wannan mataki da matsaya tasu.




Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai tsarki a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; majalisar dinkin duniya ta yi amanna da yi wa likitocin nan su ashirin shari'a a gaban kotun farar hula bat a soji ba bayan da ta soki matakin yi masu shari'a a gaban kotun soji a baya amma matsin lamba da suka ya sa mahukumtan da gwamnatin Bahrain canja wannan mataki da matsaya tasu.Babban sakataren majalisar dinkin duniya Ban Kimoon da kansa ya nuna rashin jin dadinsa da adawa da duk wani mataki na gurfanar da wadannan likitoci da suka yi wa fararen hula magani a gaban kotin soji a maimakon duk laifin da ake zarginsu a gurfanar da su a gaban kotun fararen hula lamarin da ake ganinsa bay a rasa nasaba da siyasa da mulkin kama karya da danniya da babakere da kuma wuce gonad a iri.

875442