IQNA

Ci Gaba Da Zanga-Zangar Kymar Gidan Sarauta A kasar Bahrain

13:35 - October 10, 2011
Lambar Labari: 2202326
Bangaren kasa da kasa, dubban daruruwan mutane na ci gaba da gudanar da zanga-zangar la'antar gidan sarautar Ali-khalifa a kasar Bahrain saboda zalunci da danniyarsu kan al'ummar kasar, musamman ma a cikin 'yan lokutan nan da suke murkushe fararen hula masu neman sauyi.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwea na yanar gizo cewa, dubban daruruwan mutane na ci gaba da gudanar da zanga-zangar la'antar gidan sarautar Ali-khalifa a kasar Bahrain saboda zalunci da danniyarsu kan al'ummar kasar, musamman ma a cikin 'yan lokutan nan da suke murkushe fararen hula masu neman sauyi ta fuskacin mulki da demokradiyya a kasar.

Wani rahoton kuma ya ce jaridar Daily Telgraf ta kasar Birtaniya ta habarta cewa gwamnatin Birtaniya ce ta horar da sojojin Saudiyya da suke murkushe fararen hula masu zanga-zangar lumana a kasar Bahrain.
Jaridar ta bayyana hakan ne a cikin bugunta na jiya Juma'a, bayan da karamin minista a ma'aikatar tsaron kasar ta Birtaniya Nick Harvey ya fito fili ya tabbatar da cewa; su ne suka horar da dakarun Saudiyya da suke gadin masarautar kasar, wadanda kuma su ne aka tura zuwa kasar Bahrain domin kare masarautar kasar daga boren al'umma, inda yanzu haka suke ci gaba da yin kisan gilla a kan fararen hula masu zanga-zangar lumana domin neman sauyi a cikin harkokin mulkin kasar.
Jaridar Telgraf ta ce tun kafin wannan lokacin an yi ta zargin cewa Birtaniya tana da hannu a murkushe zanga-zangar neman sauyi a kasashen Bahrain da Saudiyya, wanda hakan ke nuna irin siyar harshen damo da kasar ke bi kan batutuwa da suka shafi boren al'ummomin larabawa, inda take mara baya kai tsaye ga gwamnatocin Saudiyya da Bahrain, a bangare guda kuma tana adawa da gwamnatin Syria saboda wasu dalilai na siyasa.
876033

captcha