IQNA

Fitar Shugaban Yemen Daga Kasar Na Nuni Da Kusantowar Nasara

16:19 - October 11, 2011
Lambar Labari: 2203182
Bangaren kasa da kasa, fitar shugaba Ali Abdallah Saleh na kasar Yemen daga kasar na nuni da kosantowar nasarar masu bore, wadanda suka bayar da jininsu domin daukakar wannan al'umma wadda ke fuskantar zalunci da danniya.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto aga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Al-alam cewa, wani daga cikin fitattun 'yan adawar kasar Yemen kuma mai kare hakkokin bil adama ya sheda cewa fitar shugaba Ali Abdallah Saleh na kasar Yemen daga kasar na nuni da kosantowar nasarar masu bore, wadanda suka bayar da jininsu domin daukakar wannan al'umma wadda ke fuskantar zalunci da danniya daga wannan shugaba dan kama karya.

Bayanin ya ci gaba da cewa Dubun dubatar mutane ne suka gudanar da zanga-zanga a birnin Sana'a na kasar Yemen a wannan talata inda suke neman kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya da ya fitar da kudurin nuna goyon baya ga al'ummar kasar da ke adawa da gwamnatin kama karya ta Ali Abdallah Saleh.

Zanga-zangar ta yau dai ta zo ne a daidai lokacin da Manzon Majalisar Dinkin Duniya Jamal Ben Omar yake gabatar da wani rahoto ga majalisar ta dinkin duniya dangane da yadda lamurra ke gudana a kasar, inda kuma ake sa ran majalisar za ta fitar da wani kuduri mai yin suka ga gwamnatin ta Abdallah Saleh.

Duk da cewa a shekaranjiya asabar ne Ali Abdallah Saleh ya fito ya sanar da aniyarsa ta sauka daga kan karagar mulkin kasar a cikin kwanuka masu zuwa, to amma masu zanga-zangar sun bayyana kalaman na shugaban kasar da cewa wani salo ne na farfagandama.

877191


captcha