IQNA

Jami'an Tsaron Saudiyya Sun Gewaye Yankunan 'yan Shi'a A Gabacin kasar

16:20 - October 11, 2011
Lambar Labari: 2203183
Bangaren kasa da kasa, daruruwan motoci masu sulke na mahukuntan kasar Saudiyya sun yi wa yankin Qatif na gabacin Saudiyya da ke mazauna akasari mabiya mazhabar shi'a suke rayuwa, lamarin da ya yi sanadiyar jefa fararen hula cikin firgici.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Al-alam da ke watsa shirinsa daga birnin Tehran cewa, daruruwan motoci masu sulke na mahukuntan kasar Saudiyya sun yi wa yankin Qatif na gabacin Saudiyya da ke mazauna akasari mabiya mazhabar shi'a suke rayuwa, lamarin da ya yi sanadiyar jefa fararen hula cikin firgici da halin rashin tabbas.

Bayanin ya ci gaba da cewa Yunkurin al'umma na farkawar musulmi da ya ke kan ganiyarsa a cikin kasashen yankin gabasa ta tsakiya,ya fara kwankwasa kofofin kasar Saudiyya. Kasar ta Saudiyya wacce ta kasance cikin sukuni na wani lokaci, a wannan lokacin ta fara jin tasirin yunkurin al'umma da ya ke faruwa a cikin kasashen larabawa. Taho mu gamar da aka yi a garin al-awamiyyha a gabacin kasar tsakanin mazaunansa da mafi yawancinsu mabiya mazhbar ahlul Bayti ne da kuma jami'an tsaro, yana a matsayin wata karaurawa ce ta hatsari ga mahukuntan kasar.

Rahotannin da su ke fitowa daga garin al'awamiyyah da ke yankin Qatif a gabacin Saudiyya sun ambaci yadda mutane su ka yi zanga-zangar lumana wacce ta sauye zuwa dauki ba dadi saboda shigar jami'an tsaro. Adadin mutane da su ka jikkata kuwa a wannan taho mu gamar sun kai 24.

Domin karkatar da hankulan mutane daga hakikanin abinda ya ke faruwa a kasa, ma'aikatar harkokin cikin gidan Saudiyya ta danganta abinda ya ke faruwa da cewa kasashen waje ne su ka ingiza shi.

Kungiyar kare hakkin bil'adama ta musulunci mai cibiya a birnin London ta fitar da rahoto a ranar 4 ga watan nan na Oktoba da aciki ta bayyana cewa a cikin kasar Saudiyya ana tsare da fursunonin siyasa da adadinsu ya haura 30,000 kuma kungiyoyin kasa da kasa sun mance da su. Rahoton ya kuma ci gaba da cewa kama 'yan hamayyar siyasa a cikin Saudiyya wani abu ne da ya zama ruwan dare wanda kuma ya shafi kowane bangare na kasar ba tare da togiya ba.

877159

captcha