IQNA

Haramtacciyar Kasar Isra’ila Ce Da Keda Alhakin Harin Da Aka Kai A Yafa

20:21 - October 11, 2011
Lambar Labari: 2203261
Bangaren kasa da kasa, kungiyar gwagwarmayar palastinawa ta Hamas ta dora alhakin harin da aka kai kan palastinawa a yankin yafa a kan haramtacciyar kasar Isra’ila wadda take bayar da cikkaiyar kariya ga yahudawa ‘yan kaka gida da suke tsokanar palastinawa mazauna wadannan yankuna.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo na Palastine Info cewa, a cikin wata sanarwa da ta fitar kungiyar gwagwarmayar palastinawa ta Hamas ta dora alhakin harin da aka kai kan palastinawa a yankin yafa a kan haramtacciyar kasar Isra’ila wadda take bayar da cikkaiyar kariya ga yahudawa ‘yan kaka gida da suke tsokanar palastinawa mazauna wadannan yankuna kamar yadda sojojin yahudawan a cikin shirin yaki suke yi musu rakiya.
Bayanin ya ci gab ada cewa, tun kafin wannan lokacin yahudawan sahyuniya masu tsatsauran ra’ayi suna kai hare-hare da bindigogi da wukake kan fararen hula palastinawa marassa kariya da suke zaune a cikin yankunansu, a wasu lokutan ma har a cikin gidajensu, domin kawai su tanka sai a dora musu alhakin cewa ba su son zaman lafiya.
A jiya ne kungiyar gwagwarmayar palastinawa ta Hamas ta dora alhakin harin da aka kai kan palastinawa a yankin yafa a kan haramtacciyar kasar Isra’ila wadda take bayar da cikkaiyar kariya ga yahudawa ‘yan kaka gida da suke tsokanar palastinawa mazauna wadannan yankuna da suke cikin gabar yamma ta kogin Jordan.
876955

captcha