IQNA

An Raba Kofin Fim Din Wilatul Ishk Mai Dauke Da Tarjama Cikin Tailandanci

Bangaren siyasa da zamantakewa: fim din wilayatul Ishk da ke bayani a takaice kan rayuwar Imam Rida (AS) an raba kofin fim din da ke dauke da tarjama a cikin yaren Tailand ga mazauna Bankuk fadar mulkin kasar ta Tailand.



Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai tsarki a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; fim din wilayatul Ishk da ke bayani a takaice kan rayuwar Imam Rida (AS) an raba kofin fim din da ke dauke da tarjama a cikin yaren Tailand ga mazauna Bankuk fadar mulkin kasar ta Tailand. A ranar sha bakwai ga watan Mehir na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya ne a daidai lokacin zagayowar ranar da aka haifi Imam Rida (AS) aka raba fim din Wilayatun Ishk mai dauke da tarjamarta a cikin yaren Tailand ga mutanan wannan birnin kuma wannan fim din tana bayani ne a takaice dangane da rayuwar Imam Rida (AS) da makirci da zaluncin da ya fuskanta daga Ma'amun.


877519