Bangaren kasa da kasa:wani bangare nay an jarida da ma'aikatan kafafen watsa labarai da masu daukan hotuna na kasar Labanon sun aike da wata wasika ga sakatariyar shirya taron kafafen watsa labarai da siyasa inda a cikin wasikar suka nuna rashin dadinsu na kin halaratar wannan taro na birnin Burksel fadar mulkin Beljik saboda kasancewa tawaga daga Haramtacciyar kasar Isra'ila za ta halarci wannan taro.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai tsarki a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; wani bangare nay an jarida da ma'aikatan kafafen watsa labarai da masu daukan hotuna na kasar Labanon sun aike da wata wasika ga sakatariyar shirya taron kafafen watsa labarai da siyasa inda a cikin wasikar suka nuna rashin dadinsu na kin halaratar wannan taro na birnin Burksel fadar mulkin Beljik saboda kasancewa tawaga daga Haramtacciyar kasar Isra'ila za ta halarci wannan taro.Daga cikin yan jaridar da suka kauracewa halartar wannan taro akwai yan jarida da masu daukan hoto daga Almanar da jaridun Alsafir da Al'akhabar da gidan talbijin na Jadid a Labanon inda suka ce: mun ji dadi da aka gayyace mu a gurin wannan taro kuma muna godiya amma a bana mun samu labarin a karon farko akwai tawaga daga Haramtacciyar kasar Isra'ila da za ta halarci wannan taron saboda haka za mu kauracewa wannan taro.
877967