Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai tsarki a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; a kasuwar baje koli ta kasa da kasa a karo na sattin da uku a birnin Farnkport an ware daki na musamman dangane da siyasar waje ta Ahmadi Najad da aka bawa taken tasirin da yayi a siyasar waje.Wannan littafi da aka nuna a wajan wannan kasuwar baje koli ta birnin Frankport ya kumshi harsuna guda uku Farisanci,Turancin Ingilishi da Faransanci da kuma ya yi bayani kan siyasar Ahmadi Najad a waje da kuma mahanga da tasirin jamhuriyar musulunci ta Iran a harkokin siyasar waje.
877583