IQNA

An Tarjama' Littafin Bi'isat Wa Jihan Digar A Cikin Harshen Jamusanci

16:35 - October 12, 2011
Lambar Labari: 2203912
Bangaren al'adu da fasaha; an watsa bayan an tarjama littafin bi'isat wa jihan digar a cikin harshen Jamusanci da Said Nurusi ya wallafa.

Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai tsarki a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; an watsa bayan an tarjama littafin bi'isat wa jihan digar a cikin harshen Jamusanci da Said Nurusi ya wallafa.Wannan littafi day a kumshi shafuka dari da sattin da hudu yana bayani ne kan Lahira da tashin kiyama da kuma lada da azaba da kuma yadda mutane salihai da mabannata za su samu kansu a wannan rana wasu na cikin ni'ima da wadata wasu kuma suna cikin fuskantar azaba sakamakon ayyukan da suka aikata a wannan duniya kamar yadda suma wadanda suke cikin sa;ada da jin dadi sun samu haka ne sanadiyar ayyukan da suka aikata na alheri.


877579
captcha