Bangaren al'adu da fasaha; an samu tunani na bai daya da fahimtar juna a tsakanin marubuta da manazarta musulmi da suka halarci taro baje kolin littafai na kasa da kasa da aka gudanar a Frankfort tare da gabatar da jawabi da babban sakataren kula da tarurruka na kasa da kasa na marubuta a ranar ashirin da uku ga watan Mehir na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai tsarki a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; an samu tunani na bai daya da fahimtar juna a tsakanin marubuta da manazarta musulmi da suka halarci taro baje kolin littafai na kasa da kasa da aka gudanar a Frankfort tare da gabatar da jawabi da babban sakataren kula da tarurruka na kasa da kasa na marubuta a ranar ashirin da uku ga watan Mehir na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya.A wajan wannan taro marubuta musulmi za su yi tattaunawa ta fahimtar juna da kuma yadda za su ciyar da wannan aiki nasu mai muhimmanci na taimakon jama' da ilmantarwa gaba .Kuma wadannan marubuta musulmi za su yi iyakacin kokarinsu na ganin sun hada kansu da kafa kungiyarsu mai karfi.
877570