Bangaren kasa da kasa: kimanin masallatai dari hudu a yankin da ke cin gashin kansa ta fuskar karatu a Ningashiya a arewa maso yammacin Cana sun samu dakin karatu.
Kamfanin dillancin lbarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; kimanin masallatai dari hudu a yankin da ke cin gashin kansa ta fuskar karatu a Ningashiya a arewa maso yammacin Cana sun samu dakin karatu. Wadannan dakunan karatu da aka bude a cikin wadannan masallatai har guda dari hudu a wannan yanki na kasar Cana wata dama ce babba ga musulmin kasar da kuma hatta wadannan ba musulmi ban a samin ilimi na addinin musulunci da al'adu da hakkoki ga mabiya addinin musulunci kuma kimanin kofin littafai dubu hamsin ne aka jibge a cikin wadannan dakunan karatu.
878612