IQNA

LiTtafan Koyar Da Musulunci Sun iSa Makarantu A Filland

Bangaren kasa da kasa: Littafin koyar da addinin musulunci a karon farko ya shiga cikin tsarin koyarwa a makarantun Filland.



Kamfanin dillancin lbarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; Littafin koyar da addinin musulunci a karon farko ya shiga cikin tsarin koyarwa a makarantun Filland.An nakalto ne daga majiyar labarai ta Islam Today cewa littafan a matakin farko za a fara koyar da yara yan aji na farko da na biyu a cikin tsarin karatun kasar kuma wannan wani mataki ne na ganin an binkasa da habaka tsarin karatu a kasar da kuma bawa musulmi dama da yancin sanin ilimin addini musamman yara kanana a matsayinsu na manyan gobe kuma gimshikin ci gaba da dawwamar al'umma.



878415