Bangaren kasa da kasa: a ranar sha tara ga watan Meher na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tsi'in hijira shmasiya ne tare da halartar shugaban komitin zartarwa na kungiyar gwagwarmaya ta Hizbullahi a kasar ta labano a yankin Allailki na birnin Bairut aka bude babbar cibiyar al'adu ta Imam Rida (AS).
Kamfanin dillancin lbarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; a ranar sha tara ga watan Meher na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tsi'in hijira shmasiya ne tare da halartar shugaban komitin zartarwa na kungiyar gwagwarmaya ta Hizbullahi a kasar ta labano a yankin Allailki na birnin Bairut aka bude babbar cibiyar al'adu ta Imam Rida (AS).Kamar yadda aka nakalto daga jaridar Al'intikad da ake buga ta a kasar Labanon ta bayyana cewa; wannan cibiya tana daga cikin jerin shirye-shirye a kasar ta labanon a dalilin zagayowar irin wannan rana ta haihuwar Imam Rida (AS) karkashin sa ido na Said Hashim Safawi Aldine shugaban komitin zartarwa na kungiyar Hizbullahi.
878564