IQNA

An Yiwa Wani Malamin Shi'a Kisan Gilla A Karbala

Bangaren kasa da kasa: Muhind Mu'amar Abu Zainab daya daga cikin malaman shi'a kuma fitattu a birnin Karbala a safiyar ranar sha tara ga watan Meher na shekara ta dubu daya da dari uku da tsi'in hijira shamsiya wasu mutane dauke da makamai suka yi masa kisan gilla a yankin Shuhada'a Saif Saad a gabacin birnin Karbala'.



Kamfanin dillancin lbarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; Muhind Mu'amar Abu Zainab daya daga cikin malaman shi'a kuma fitattu a birnin Karbala a safiyar ranar sha tara ga watan Meher na shekara ta dubu daya da dari uku da tsi'in hijira shamsiya wasu mutane dauke da makamai suka yi masa kisan gilla a yankin Shuhada'a Saif Saad a gabacin birnin Karbala'a.Bayan sllar magariba da isha'I ne wasu suka bude masa wuta a kan hanayar ta komawa gida tare da shi da diraebansa inda kuma ya yi shahada safiyar daren da aka bude masu wuta lamarin da ke nuni da Karin tabarbarewar tsaro da yawaitar kisan gilla a wannan kasa ta Iraki.

878409