IQNA

Bincike Kan daftarin Kuduri Kan Abdalla Salihi A Komitin Tsaro

Bangaren kasa da kasa: Britaniya ta gabatar da wani daftarin kuduri kan dan kama karya shugaban kasar yaman Abdalla Salih kuma a yau ne komitin tsaro na majalisar dinkin duniya zai fara zamansa kan wannan bukata.





Kamfanin dillancin lbarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; Britaniya ta gabatar da wani daftarin kuduri kan dan kama karya shugaban kasar yaman Abdalla Salih kuma a yau ne komitin tsaro na majalisar dinkin duniya zai fara zamansa kan wannan bukata.Akwai komiti da dama day a gudanar da bincike kan abubuwan da suka faru a kasar ta Yamen da kuma zai gabatar da sakamakon binciken da kuma za a tattauna kan wannan daftarin kuduri da kasar Britaniya ta gabatar sai dai wani lamari mai sa ayar tambaya kan wannan lamari shi ne yadda tun da jimawa gwamnatin Abdalla Salih ke kisa da gallazawa al'ummar kasar ta Yamen amma mai ya sa wannna jinkiri kuma sai yanzu ne za a fara tattaunawa daftarin kuduri kansa kuma ina ne kudurin zai kai .


878368