Bangaren kasa da kasa; a karon farako Vatikan ta dauki bakuncin gudanar da baje kolin kasa da kasa na nuna kwarewa ta fuskar rubutun musulunci da aka bawa taken nuna kauna ga Ma'aikin Allah Muhammad Dan Abdullahi Tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa tsarkaka.
Kamfanin dillancin labaran Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: a karon farako Vatikan ta dauki bakuncin gudanar da baje kolin kasa da kasa na nuna kwarewa ta fuskar rubutun musulunci da aka bawa taken nuna kauna ga Ma'aikin Allah Muhammad Dan Abdullahi Tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa tsarkaka.wanann wani mataki ne na jinjinawa da kuma yabo domin ko ba komi zai kara kusanci da kaunar juna a tsakanin musulmi da kiristoci a fadin duniya da isar da sako ga makiyansu masu son haddasa fitina da rikici a tsakaninsu domin cimma wata manufa tasu ta boye.
880531