IQNA

Wani Musulmi Marubuci Dan kasar Algeria Ya Samu Lambar Yabo Ta Frankfort

14:08 - October 18, 2011
Lambar Labari: 2207299
Bangaren kasa da kasa, wani musulmi marubuci dan kasar Algeria, ya samu wata lambar yabo da Frankfort da ake bayarwa akasar jamus, saboda gagarumar rawar da yake takawa wajen kawo zaman lafiya a tsakanin al’ummomin duniya.
Kamfanin diallncin labaran iqna ya habarta cewa, ya samu wani bayani daga shafin sadarwa na yanar gizo na dna-algerie cewa, Bu Allam Sansal wani musulmi marubuci dan kasar Algeria, ya samu wata lambar yabo da Frankfort da ake bayarwa akasar jamus, saboda gagarumar rawar da yake takawa wajen kawo zaman lafiya a tsakanin al’ummomin duniya musamman ma tsakanin musulmi da wadanda ba musulmi ba.
Bayanin ya ci gaba da cewa, mutumin ya samu wannan kyautar ne bisa namijin kokarin da ya yi a cikin dukaknin rubuce-rubucensa kan lamurra na zamantakewar al’umma, inda ya yi kokarin nuna ma sauran al’ummomi da mabota addinai cewa, addinin musulunci na zaman lafiya ne da fahimtar juna tsakaninsa da sauran addinai.
Haka nan kuma ya nuna goyon bayansa ga mikewar da kasashen larabawa suka yi wajen tunkarar azzaluman shugabanni yan kama karya acikin kasashensu, lamarin da ke tabbatr da cewa shi mai son asdalci ne a tsakanin mutane kamar yada mutane da dama suka bayar da sheda kan haka.
881430




captcha