Bangaren kasa da kasa: daya daga cikin yariman kasar Saudiya ya danganta fasadin da ke yaduwa a tsakanin kasashen larabawa da cewa ya samo asali ne daga fasadin mahukumtan Saudiya wadanda bas u damuwa da halin da al'ummominsu ke ciki na kunci da wahalhalu musamman idan aka yi la'akari da halin da al'ummomin yankin ke ciki.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: daya daga cikin yariman kasar Saudiya ya danganta fasadin da ke yaduwa a tsakanin kasashen larabawa da cewa ya samo asali ne daga fasadin mahukumtan Saudiya wadanda bas u damuwa da halin da al'ummominsu ke ciki na kunci da wahalhalu musamman idan aka yi la'akari da halin da al'ummomin yankin ke ciki.Tasma Bint Sa'ud Bin Abdul Aziz a ranar ashirin da hudu ga watan Meher na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in ne hijira shamsiya a wata tattaunawa da ta yi da gidan talbijin din Al'alam ta bayyana cewa: ta yi amanna fasadin da ke faruwa a kasashen yankin ya samo asali ne daga kasar Saudiya tare da jaddada cewa gwamnatin saudiya dole ta nuna adalci a kasar Bahrain da Yaman da gudanar da siyasar baidaya a fadin yankin ba tare da nuna bambanci ba.
881315