IQNA

An Tabbatar Da Kisan Dan Kaddafi

15:23 - October 18, 2011
Lambar Labari: 2207412
Bangaren kasa da kasa; An kashe Khamis karamin dan Mu'ammar Khaddafi a ranar alhamis.


Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: Tashar telbijin din al-Ra'ay, mai kusanci da hambararren shugaban kasar Libya Mu'ammar Khaddafi ta sanar da mutuwar karamin dansa Khamis a ranar alhamis din da ta gabata.
Labarun da tashar ta watsa ya ce, an kashe khamis ne a yayin fada da sojojin gwamnatin rikon kwarya a yankin Tarhuna mai nisan kilo mita 80 daga birnin Tripo a ranar alhamis din da ta gabata.
Wannan dai shi ne karon farko da wata kafa mai kusanci da hambararren shugaban na kasar Libya ta tabbatar da mutuwar khamis.




881293
captcha