Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci tai ran ne ya watsa rahoton cewa : ma'aikatar Harkokin wajan Faransa a ranar ashirin da biyar ga watan Meher na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya sun bude wani bangare da ajiyar labaran da suka shafi ayyukan hajji a cikin shafinsu na Internet.Kakakin ma'aikatar harkokin wajan kasar Faransa a wata tattauanawa da manema labarai ya bayyana cewa; burin bude wannan shafi day a kumshi bayanai da labarai kan ayyukan hajji ga musulmin kasar Faransa wata dama ce ta samin labarai kan mahajjatan kasar Faransa da suka tafi kasar Saudiya domin sabke farali.Duk da cewa wannan shi ne matakin farko da ma'aikatar ta bullo da irin wannan tsari to amma zai taimaka matuka gaya musamman ga musulmi da bayar da yancinsu.
882070