Bangaren kasa da kasa, daya daga cikin jagororin 'yan tawayen kasar Libya da suke dauke da makamai ya ce mayakansa sun gano wurin da Gaddafi yake boye a cikin birnin Sirte kuma nan bad a jimawa ba za a kame shi.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto wani rahoto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din al-alam cewa, daya daga cikin jagororin 'yan tawayen kasar Libya da suke dauke da makamai ya ce mayakansa sun gano wurin da Gaddafi yake boye a cikin birnin Sirte kuma nan bad a jimawa ba za a kame shi domin gurfanar da shi a gaban shari'a.
Dan tawayen ya ci gaba da cewa suna samun babbar galaba kan dakarun da suke yin biyayya ga kanar gaddafi a garuuwan Sirte da kuma Bani walid, inda y ace a halin kusan dai an kammala kwace birnin daga hannun dakarun Gaddafi, kuma za a tabbatar da doka da oda a birnin baki daya.
Rahoton ya kara da cewa daya daga cikin jagororin 'yan tawayen kasar Libya da suke dauke da makamai ya ce mayakansa sun gano wurin da Gaddafi yake boye a cikin birnin Sirte kuma suna sa ran samun nasarar damke shi da zaran sun isa gare shi a cikin 'yan kwanaki masu zuwa.
882531