Bangaren kasa da kasa, babban jami'in da ke kula da harkokin aikin hajji a kasar saudiyya Khalid Faisal ya bayyana cewa a ci gaba da bunkasa ayyukan hajji na bana an kara fadada birnin Mina ta yadda zai samu daukar mutane da dama.
Kamfanin diallncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ma'aikatar hajji a saudiyya cewa, babban jami'in da ke kula da harkokin aikin hajji a kasar saudiyya Khalid Faisal ya bayyana cewa a ci gaba da bunkasa ayyukan hajji na bana an kara fadada birnin Mina ta yadda zai samu daukar mutane da dama bisa la'kari da karuwar mahajjata.
A kowace shekara dai gwamnatin kasar saudiyya kan kayyade adadin mutanen da za su halarci aikin hajji daga dukaknin kasashen duniya, inda kasashne musulmi na gabacin Asia da Afirka ne suka yawan mahajjata a kowace shekara, kamar dai yadda alkalumman kidayar alhazai suka nuna.
A kan haka ne babban jami'in da ke kula da harkokin aikin hajji a kasar saudiyya Khalid Faisal ya bayyana cewa sun ci gaba da bunkasa ayyukan hajji na bana, kuma sun kara fadada birnin Mina ta yadda zai samu daukar mutane da dama da suke gudanar da ayyukan hajji.
882317