IQNA

Za A Gudanar Da Zaman Taro Na Kafofin Sadarwar Musulunci A Jakarta

14:42 - October 20, 2011
Lambar Labari: 2208450
Bangaren kasa da kasa, kwamitin kafofin sadarwa na kasashen musulmi zai gudanar da wani zama na kasa da kasa akaro na biyu a birnin Jakarta na kasar Indonesia tare da hadin gwiwa da ma’aikatar kula da harkokin addini ta kasar.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo na Nasij cewa, kwamitin kafofin sadarwa na kasashen musulmi zai gudanar da wani zama na kasa da kasa akaro na biyu a birnin Jakarta na kasar Indonesia tare da hadin gwiwa da ma’aikatar kula da harkokin addini ta kasar a cikin wata mai zuwa.
Abdullah Ibn Muhsin babban sakataren kwamitin ya bayyana cewa, sun shirya gudanar da wannan zaman taron saboda matsalolin da kasashen musulmi suke ciki da kuma barazanar da ake yi wa muuslmi a kowane lokaci, da kuma yadda ya kamata musulmi su dauki matakan kare kansu ta hanyar kafofin sadarwarsu.
Yanzu haka dai kwamitin kafofin sadarwa na kasashen musulmi zai gudanar da wani zama na kasa da kasa akaro na biyu a birnin Jakarta na kasar Indonesia tare da hadin gwiwa da ma’aikatar kula da harkokin addini a Idonesia, tare da halartar wakilai mambobin kwamitin daga kashen musulmi daban-daban.
883056





captcha