Kmafanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na lorientlejour cewa, Ahmad Tayyib babban malamin jami’ar Azhar ta kasar Masar ba zai halarci taron da aka shirya gudanarwa na tattaunawa kan addinai a kasar Italia ba a cikin makon mai zuwa, kamar dai yadda shugaban kwamitin tattaunawar addinai na fadar Vatican ya fada a wata zantawa da ta hada shi da manema labarai a birnin Rom.
Ya ce babban dalilin da ya sanya baban malamin jamiar Azahar ba zai halarci zaman taron ba shine, furucin da paparoma ya yi a kwanakin baya da ke cewa mabiya addainin musulunci suna danne kiristoci da suke rayuwa acikin kasashen musulmi, tare da takura musu da kuma hana su bin tafarkin addininsu, wanda hakan ya bakanta wa malaman Azhar, inda suke yanke dangantaka da Vatican.
Har yanzu dai babu wata dangantaka tsakanin jami’ar Azhar da kuma fadar Vatican sakamakon wannan furuci na rashin adalci da rashin tunanin na basira, wanda ya fito daga bakin mutumin da ake kallo a matsayin shugaba kum ajagora na mabiya addinin kirista.
Dr. Ahmad Tayyib babban malamin jami’ar Azhar ta kasar Masar ba zai halarci taron da aka shirya gudanarwa na tattaunawa kan addinai a kasar Italia ba a cikin makon mai zuwa, kamar dai yadda shugaban kwamitin tattaunawar addinai na fadar Vatican ya furta. 882999