IQNA

Nasarar Da hamas ta Samu A Musayar Fursunoni Sakamako Ne Na Gwagwarmaya

14:44 - October 20, 2011
Lambar Labari: 2208452
Bangaren kasa da kasa, nasarar da kungiyar gwagwarmayar musulunci ta palastinawa Hamas ta samu sakamakon musayar fursunoni tsakaninta da haramtacciyar kasar Isra’ila, sakamako ne na gwagwarmayar al’ummar palastinu ta neman ‘yanci.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Almanar da ke watsa shirye-shiryenta daga birnin Beirut na kasar Lebanon cewa, shugaban bangaren siyasa na kungiyar Hamas Khalid Mush’al ya bayyana cewa nasarar da kungiyar gwagwarmayar musulunci ta palastinawa Hamas ta samu sakamakon musayar fursunoni tsakaninta da haramtacciyar kasar Isra’ila, sakamako ne na gwagwarmayar al’ummar palastinu ta neman ‘yanci daga zalunci da danniyar yahudawan sahyuniya.
Khalid Mash’al ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da wani jawabi a gaban manema labarai a birnin Alkahira na kasar Masar dangane da yadda musayar fursunonin palastinawa da sojan haramtacciyar kasar Isra’ila guda ta wakana tsakanin kungiyar hamas da kuma haramtacciyar gwamnatin yahudawan sahyuniya.
Mash’al ya ce nasarar da kungiyar gwagwarmayar musulunci ta palastinawa Hamas ta samu sakamakon musayar fursunoni tsakaninta da haramtacciyar kasar Isra’ila, sakamako ne na gwagwarmayar al’ummar palastinu da yahudawan sahyuniya da suka mamaye musu kasa.
882943

captcha