IQNA

Musulmin Kasar India Sun Yi Kira Da Ayi Hattara Da Bazuwar Akidar Wahabiyanci

14:42 - October 20, 2011
Lambar Labari: 2208454
Bangaren kasa da kasa, musulmin kasar India sun yi kira da dauki matakai na fadar da sauran musulmi kan hadarin da ketattare da yaduwar akidar wahabiyanci a cikin kasashen musulmi wanda ke karkatar da musulmi da hakikanin koyarwa ta addini.
Kamfanin diallncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto wani rahoto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar India Times cewa, babban sakataren majalisar malaman addinin muslunci a kasar India Sayyid Muhammad ashraf ya yi kira da dauki matakai na fadar da sauran musulmi kan hadarin da ketattare da yaduwar akidar wahabiyanci a cikin kasashen musulmi wanda ke karkatar da musulmi da hakikanin koyarwa ta addinin musulunci ta hakika.
Malamin ya ce idan aka yi la’akari da yadda gwamnatin wahabiyawan saudiyya take ci gaba da kutsawa cikin musulmi tare da dora su kan tafarkin tsatsauran ra’ayi, wanda hakan ke bata fuskar addinin muslunci a idon sauran al’ummomin mutanen duniya da mabiya addinai.
Ya ce dole ne musulmi su zama cikin fadaka kan hadarin akidar wahabiyanci a cikin muslmi, domin kuwa akida ce ta yi hannun riga da koyarwa irin ta addinin muslunci baki daya, kuma ta hanayar hakan ne makiya suke samun damar bakanta sunan musulunci, tare da bayyana musulmi a matsayin ‘yan ta’adda.
883020


captcha