Kamfanin diallncin labaran iqna ya habarta cewa, ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo na naharnet.com cewa wata tawaga daga kasar Lebanon ta nufi kasar Libya domin neman bayanai dangane da makomar Imam Musa Sadr wanda tsohon shugaban mulkin kama karya na kasar Libya ya boye batunsu sama da shekaru talatin da uku da suka gabata bayan da aike masa da goran gayyata tare da wasu masu rufa masa baya su biyu.
A ranar Alhamis da ta gabata ne ‘yan tawayen kasar Libya suka halaka Gaddafi, amma a nasa bangaren kwamitin kare hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya ya bukaci da a gudanar da bincike kan musabbabin mutuwar tsohon jagoran kasar Libya Mu'ammar Gaddafi bayan kama shi da ransa.
Mai Magana da yawun kwamitin ne ya bayyana hakan a yau, inda ya ce akwai bayanai masu karo da juna dangane da mutuwar Gaddafi, domin kuwa dukkanin bayanai da ma hotunan bidiyo da aka dauka sun tabbatar da cewa an kame shi ne da ransa, a lokaci guda kuma sai ga shi matacce tsakanin wadanda suka kame shi, ya ce idan an kasha Gaddafi ne bayan kame shi da ransa, wannan lamari ne mai matukar hadari bisa dokokin kasa da kasa.
Wani likita mai suna Ibrahim Tika da ya duba gawar kanar gaddafi a garin Misrata ya bayyana cewa, Gaddafi ya mutu ne ta hanyar harbi da harsasan bindiga a tsakiyar cikinsa da kuma kan goshinsa. A nata bangaren mai dakin kanar Gaddafi ta bukaci majalisar dinkin duniya da ta gudanar da bincike kan mutuwar mijinta da kuma danta Mu'tasim, wadanda aka kama su da ransu daga bisani kuma aka ga gawawwakinsu cikin jinni.
884010