Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto rahoto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin dil Al-alam cewa dubban daruruwan mutane sun gudanar da wata gagarumar zanga-zanga a jiya wadda suka kira da juma’ar nasara a kasar Yemen inda suke shugaban kasar Ali Abdallasaleh da ya gaggauta yin murabus ba tare da wani bata lokaci, tun kafin damar yin hakan cikin ruwan sanyi ta kubuce masa.
Wasu rahotannin kuma sun ce akalla mutane uku ne su ka rasa rayukansu a wani fada tsakanin kabilun da su ke goyon bayan shugaban kasar Yamen Ali Abdallah Saleh da masu adawa da shi.
Rahotannin da su ke fitowa daga Yamen sun ce an rika yin musayar wuta a yankunan Husbah da Sufan a cikin birnin Sanaa.
Wata majiya ta kusa da shugaban kabilar Hashid al-Ahmar ta tabbar da kashe mutane kuma wasu mutanen 18 su ka jikkata, a cikin kwanaki uku a jere an kashe mutane 26 a taho mu gama din da ake yi tsakanin masu goyon bayan Ali Abdallah Saleh da kuma masu adawa da shi, a yau juma'a ne dai kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya zai yi zama na musamman domin tattauna makomar kasar Yamen.
884006