Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya naklato dagashafin sadarwa na yanar gizo na alwefaq cewa, fitacciyar jam’iyyar siyasa ta kasar Bahrain ta Al-wifaq ta bayyana cewa halakar tsohon shugaban mulkin kama karya na kasar Libya babban sako ne shugabanni ‘yan mulkin kama karya da danniya, da ke tabbatar musu da cewa makomarsu ba za ta yi kyau ba.
Wasu bin diddigin abin da ke faruwa dai suna ganin cewa, kashe hambararren shugaban kasar Libya Muammmar Gaddafi da yan juyin juya hali suka yi a jiya Alhamis bayan fafutukar kifar da gwamnatinsa da ta shafe watanni 8, ya kawo wa alummar Libya farin ciki da murnar rabuwa da mai mulkin kama-karya wanda ya shafe watanni biyu yana buya domin tsirar da ransa.
Muammar Gaddafi wanda ya rayu shekjarui 69 a duniya ya shugabanci kasar Libya na tsawon shekaru 42, amma watanni takwas da suka gabata ya fuskanci zanga zangar da ba a taba ganin irinta ba a kasar Libya wanda sakamakon haka aka tilasta masa Gaddafi tserewa daga Trabulus fadar gwamnatin kasar a watan Agusta. Daga wancan lokaci kuma Gaddafi ya yi ta buya har zuwa jiya Alhamis da mayakan juyin juya hali suka kashe shi a wani a garin Sirte inda ya fake.
Bayan bayyanar labarin mutuwar Gaddafi hukumar wucin gadin kasar da wasu bangaroein kasa da kasa sun bayyana rayoyinsu kan wannan alamri. Mataimakin shugaban hukumar wucin gadin Libya Abdulhafiz Ghuqah ya sheda wa manema labarai a birnin Tarabulus cewa: 'Muna sanar da duniya cewa mayakan juyin juya halin Libya sun kashe Gaddafi'.
884001