Bangaren kasa da kasa, Manazarta da masana harkokin siyasar kasar Libiya sun bayyana cewa: muhimman matsaloli da kalubalen da suke fuskantar kasar Libiya bayan kashe Mu'ammar Gaddafi sune; rubuta sabon kundin tsarin kasar, karbe makamai a hannun mutane, kafa sabuwar gwamnati, ficewar sojojin kungiyar tsaro ta nato.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na tashar manar cewa, shugaban jam'iyyar adalci da wanzar da tsarin dimokaradiyya a kasar Libiya Hadi Shaluf ya bayyana cewa; babban kalubalen da zasu fuskanta a Libiya a halin yanzu da gwamnatin marigayi Mu'ammar Gaddafi ta kawo karshe bayan halaka shi; shi ne matsalar rubuta sabon kudin tsarin mulkin kasar.
Shaluf ya furta cewa; a halin yanzu kasar Libiya ba tada wani tsayayyen kudin tsarin mulki, kuma duk 'yan siyasar Libiya suna son gabatar da irin shirye-shiryen da suke dauke da su na sake gina kasar a bangarori da dama da suka hada da siyasa, tattalin arziki, tsaro, zamantakewa da sauransu, amma dole ne wadannan muhimman batutuwa su kasance sun gudana ne karkashin dokokin kasa, sakamakon haka kokarin 'yan siyasar kasar a yanzu shi ne ganin an rubuta kudin tsarin mulki nan da dan wani lokaci mai zuwa da zai samu amincewar al'umma.
Shi kuwa Idris Adbish daya daga cikin 'yan siyasar kasar ta Libiya yana ganin babban kalubalen da ke gaban Libiya shi ne hanyar da za a bi wajen ganin an karbe makamai daga hannun mutanen kasar. Adbish ya kara da cewa: Dole ne a dauki matakin karbe dukkanin makamai da suke hannun mutane da suke shawagi a kan hanyoyin kasar, saboda rashin karbe wadannan makaman zai wurga tsaron kasar cikin babban hatsari.
Har ila yau a ra'ayin Idris Adbish karbe makaman dole ne ya kasance bayan kafa rundunar sojin kasa da ba a sanya batun siyasa wajen kafa ta ba.
Muhammad Mahmud As-Sharkasi masanin ilimin siyasa kuma malamin jami'an birnin Benghazi ya bayyana cewa; kafa gwamnati ita ce babbar kalubalen da kasar Libiya ke fuskanta. As-Sharkasi ya yi nuni da cewa; tsawon shekaru 40 da suka gabata babu wata rawa ta a zo a gani da al'ummar Libiya ke takawa a fuskar gudanar da harkar mulkin kasar. A tsawon wannan lokacin wasu 'yan tsiraru ne kawai ke tafiyar da mulkin kasar bisa son ransu, don haka kafa sabuwar gwamnati a Libiya tana bukatar samun kwararrun mutane masu zurfin tunani da fahimta daga dukkanin bangarorin al'ummar kasar.
Ala'u bin Dardif masanin harkokin kasa da kasa cewa ya yi babbar matsalar da kasar Libiya zata fuskanta ita ce tsoma bakin kasashen yammacin Turai a harkar cikin gidan kasar saboda ba zasu taba amincewa su saki dukiyar Libiya da ke hannunsu ba har sai an sakar musu marar tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar.
883891