IQNA

Mutanen Kasar Masar Na Yin Kira Da A Kori Jakadan Saudiyya Daga Kasar

18:41 - October 22, 2011
Lambar Labari: 2209541
Bangaren kasa da kasa, al’ummar kasar Masar na ci gaba da yin kira da a dauki kwararan matakai na ladabtar da gwamnatin wahabiyawan saudiyya ta hanyoyi da dama sakamakon shigar shugular da take cikin harkokinsu na cikin gida.
Kmafanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin dil Al-alam cewa, al’ummar kasar Masar na ci gaba da yin kira da a dauki kwararan matakai na ladabtar da gwamnatin wahabiyawan saudiyya ta hanyoyi da dama sakamakon shigar shugular da take cikin harkokinsu na cikin gida da kuma mummunar rawar da ta taka a lokacin mulkin Husni Mubara wajen cutar da mutanen Masar.
Rahoton ya ci gaba da cewa mutane da dama ne suka gudanar da zanga-zanga a birnin Alkahira suna neman mahukuntan sojin kasar da su gaggauta rufe ofishin jakadancin kasar saudiyya da ke kasar, domin kuwa babu wani da yake haifarwa in banda rikici da kawo sabani tsakanin al’ummar Masar.
Bayanin ya kara da cewa al’ummar kasar Masar na ci gaba da yin kira da a dauki kwararan matakai na ladabtar da gwamnatin wahabiyawan saudiyya ta hanyoyi da dama sakamakon shigar shugular da take cikin harkokinsu na cikin gida bugu da kari kan hakan haifar da matsaloli tsakanin musulmi da kirista.
Saudiyya dai ita ce babbar aminiyar Amurka da yahudawan sahyuniya a yankin gabas ta tsakiya bayan faduwar shugaban mulkin kama karya na kasar Masar Husni Mubarak, wanda shi ne ke kare manufofin Amurka da yahudawan sahyuniya a yankin gabas ta tsakiya baki daya.
883871


captcha