IQNA

A Jiya Ne Yarima Mai Jiran Gado Na Saudiya Ya Mutu

15:39 - October 23, 2011
Lambar Labari: 2210241
Bangaren kasa da kasa: Yarima Sultan Bin Abdul Aziz yarima mai jiran gado na kasar Saudiya ya mutu a wata asubici a birnin New York na kasar Amerika bayan fama da doguwar rashin lafiya da kuma jiya ta wani lokaci mai tsawo.

Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; Yarima Sultan Bin Abdul Aziz yarima mai jiran gado na kasar Saudiya ya mutu a wata asubici a birnin New York na kasar Amerika bayan fama da doguwar rashin lafiya da kuma jiya ta wani lokaci mai tsawo.Gidan talbijin na Al'alam da ke watsa shirye shiryensa ta hanyar tauraron dan adam daga nan birnin Tehrain na jamhuriyar musulunci ta Iran a jiya talatin ga watan meher na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya ya watsa labarin mutuwar yarima mai jiran gado na kasar Saudiya Sultan Bin Abdul Aziz dan shekaru tamanin da biyar a duniya wanda aka kai shi kasar ta Amerika a makonni biyun da suka gabata domin yi masa magani.Shi dai Sultan bin Abdul Aziz yarima mia jiran gado an haife shi ne a ranar biyar ga watan Janairu na shekara ta dubu daya da dari tara da talatin da daya miladiya kuma shi ne yake rike da ministan tsaro da sojojin sama a kasar ta Saudiya.


884211

captcha