Bangaren siyasa da zamantakewa: an gudanar da bukin yaye dalibai sattin da biyar yan kasar Tailand da suka kammala karatunsu a jami'ar musulunci ta Azhar a kasar Masar.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; an gudanar da bukin yaye dalibai sattin da biyar yan kasar Tailand da suka kammala karatunsu a jami'ar musulunci ta Azhar a kasar Masar.A ranar juma'ar da ta gabata ashirin da tara ga watan Meher na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya aka gudanar da wannan buki tare da halartar jakadan Tailand a kasar ta Masar da kuma shugabannin jami'ar ta Azhar kuma yadda jakadan ya halarci wannan taro nay aye dalibai na kasar ta Tailand ya bawa wannan buki armashi da nuna yadda yake da muhimmanci ga mahukumtan kasar ta Tailand tare da gabatar da jawabai masu gamsarwa da kuma jinjinawa daliban da suka kammala karatunsu a wannan jami'a ta Azhar a kasar ta Masar.
883849