Bangaren zamantakewa: a cikin watan Azar mai zuwa na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a jami'ar Isfahan a nan jamhuriyar musulunci za a gudanar da taron kasa da kasa na farkawar musulmi a yau tare da halartar malaman jami'a da shugabannin jami'o'I da cibiyoyin ilimi mai zurfi da kuma wakilan bangaren al'adu .
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; a cikin watan Azar mai zuwa na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a jami'ar Isfahan a nan jamhuriyar musulunci za a gudanar da taron kasa da kasa na farkawar musulmi a yau tare da halartar malaman jami'a da shugabannin jami'o'I da cibiyoyin ilimi mai zurfi da kuma wakilan bangaren al'adu .ma'aiaktar ilimi da bincike tare da hadin guiwar cibiyar al'adu da kula da shirye-shirye na zamantakewa suka shirya inda masana da malamai za su tattauna da zakulo hanyoyin kara tayar da musulmi daga barci da kuma kara wannan fadakarwa.
884555