Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo na jaridar Al-intiqad cewa, Sayyid Ali fadlollah ya bayyana cewa, yanzu ya zama wajibi kan al'ummar kasar Libya da su zama cikin fadaka dangane da makirci irin na kasashen yammacin turai bayan kawar da tsohon shugaban mulkin kama karya na kasar Libya Mu'ammar Gaddafi.
Wani masani mai suna Shaluf ya furta cewa; a halin yanzu kasar Libiya ba tada wani tsayayyen kudin tsarin mulki, kuma duk 'yan siyasar Libiya suna son gabatar da irin shirye-shiryen da suke dauke da su na sake gina kasar a bangarori da dama da suka hada da siyasa, tattalin arziki, tsaro, zamantakewa da sauransu, amma dole ne wadannan muhimman batutuwa su kasance sun gudana ne karkashin dokokin kasa, sakamakon haka kokarin 'yan siyasar kasar a yanzu shi ne ganin an rubuta kudin tsarin mulki nan da dan wani lokaci mai zuwa da zai samu amincewar al'umma.
Shi kuwa Idris Adbish daya daga cikin 'yan siyasar kasar ta Libiya yana ganin babban kalubalen da ke gaban Libiya shi ne hanyar da za a bi wajen ganin an karbe makamai daga hannun mutanen kasar. Adbish ya kara da cewa: Dole ne a dauki matakin karbe dukkanin makamai da suke hannun mutane da suke shawagi a kan hanyoyin kasar, saboda rashin karbe wadannan makaman zai wurga tsaron kasar cikin babban hatsari.
Muhammad Mahmud As-Sharkasi masanin ilimin siyasa kuma malamin jami'an birnin Benghazi ya bayyana cewa; kafa gwamnati ita ce babbar kalubalen da kasar Libiya ke fuskanta. As-Sharkasi ya yi nuni da cewa; tsawon shekaru 40 da suka gabata babu wata rawa ta a zo a gani da al'ummar Libiya ke takawa a fuskar gudanar da harkar mulkin kasar. A tsawon wannan lokacin wasu 'yan tsiraru ne kawai ke tafiyar da mulkin kasar bisa son ransu, don haka kafa sabuwar gwamnati a Libiya tana bukatar samun kwararrun mutane masu zurfin tunani da fahimta daga dukkanin bangarorin al'ummar kasar.
Ala'u bin Dardif masanin harkokin kasa da kasa cewa ya yi babbar matsalar da kasar Libiya zata fuskanta ita ce tsoma bakin kasashen yammacin Turai a harkar cikin gidan kasar saboda ba zasu taba amincewa su saki dukiyar Libiya da ke hannunsu ba har sai an sakar musu marar tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar.
884502