Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: jama'atul Ikhwanul Muslim a kasar Jodan sun fitar da wani bayani da a cikinsa suka bayyana cewa ba za su shiga cikin sabuwar gwamnatin da sabon firaminista Aun AlKhasawina zai kafa saboda bas u zaton alheri kan hakan. Ranar talatin ga watan Meher na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya Jama'atul Ikhawanul Islami a kasar Jodan ya sanar da cewa ko kusa ba za su shiga a dama da sub a a cikin sabuwar gwamnati da sabon firaminista zai kafa da hakan ke nufi sun yi watsa da tayin da sabon firaministan ya yi masu na gayyatar su shiga a cikin gwamnatin da zai kafa .
885118