Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: Taron Kasa Da Kasa Na Akadami Ulumin Jihadul Islami LAS karo na sha takwas da ake gudanarwa tun ranar talatin ga watan Maher na shekara ta dubu daya da dari uku da Tis'in hijira shamsiya a birnin Doha fadar mulkin kasar Katar.Wannan taro na kwanaki uku masana da malamai da manazarta da kuma wakilan gwamnatoci da na jama'a za su yi nazari da binciken hanyoyin binkasa harkokin ilimi a fadin kasashen musulmi da kuma binciken tarihin ilmomin musulunci da dangantakarsa da ilmomi na ma'anawiya da lamuran zamantakewa da kuma siyasa kamar kimiya da makamashi da dai sauransu.
885056