IQNA

Mutuwar Kaddafi Wata hanya Ce Ta Sakin Jagoran Yan Shi'ar Labanon

14:50 - October 24, 2011
Lambar Labari: 2210897
Bangaren kasa da kasa: shugaban ofishin siyasa na Jabahatul Amal a kasar Labanon ya yi nuni da kokarin da ak yi ba dare ba rana da kungiyarsu ke yin a ganin an sako Imam Musa Sadre bayan kasha Mu'ammar Kaddafi hambararren shugaban kasar Libiya da aka kasha wanda shi ne sanadiyar bacewar jagoran yan shi'an na kasar Labanon a daidai lokacin da yake ziyarar aiki a kasar ta Libiya.




Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: shugaban ofishin siyasa na Jabahatul Amal a kasar Labanon ya yi nuni da kokarin da ak yi ba dare ba rana da kungiyarsu ke yin a ganin an sako Imam Musa Sadre bayan kasha Mu'ammar Kaddafi hambararren shugaban kasar Libiya da aka kasha wanda shi ne sanadiyar bacewar jagoran yan shi'an na kasar Labanon a daidai lokacin da yake ziyarar aiki a kasar ta Libiya.Jamil Haik shugaban ofishin siyasa na kungiyar Amal a ranar talatin ga watan Meher na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya ne ya bayyana cewa: faduwar gwamnatin dan kama karya kuma da kasha Kaddafin da aka yi an shiga wani babu na kokarin ganin an sako jagoran yan shi'ar kasar ta Labanon Imam Musa Sadre da kuma wadanda suke tare da shi a wancen lokaci da suke ziyarar aiki a kasar ta Libiya da fatar ganin sun koma a cikin iyalansu a kasar Labanon.


885050

captcha