Bangaren kasa da kasa: Kungiyar Amal a kasar labanon ta shirya wata gagaramar tawaga da ta tashi a jiya daya ga watan Aban shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in domin isa kasar Libiya a kokarin sanin makomar Imam Musa Sadre da kuma ganin an sako shi ya koma cikin iyalanshi tare da wadanda suke tare da shi lamin lafiya.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: Kungiyar Amal a kasar labanon ta shirya wata gagaramar tawaga da ta tashi a jiya daya ga watan Aban shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in domin isa kasar Libiya a kokarin sanin makomar Imam Musa Sadre da kuma ganin an sako shi ya koma cikin iyalanshi tare da wadanda suke tare da shi lamin lafiya.Wannan gagaramar tawaga da ta tashi daga kasar ta labanon ta hada Sheikh Muhammad yakubi da Abas Badrul Dine har ila yau wasu gungun masana hakkin dan adam suna yi masu rakiya sun kama hanya a jiya domin isa kasar ta Libiya domin tattaunawa da sabbin mahukumtan kasar a kokarin ganin an sako Imam Musa Sadr wanda Kaddafi ya kama da tsare shi cikin zalunci babu labarinsa a daidai lokacin da yake ziyarar aiki a cikin kasar ta Libiya a wannan lokacin.
885002