IQNA

Al'ummar Iran Na Bukatar Sauran Al'ummomi Da Su samu Daukaka

16:34 - October 24, 2011
Lambar Labari: 2210953
Bangaren kasa da kasa, jakadan kasar Iran a kasar Lebanon ya bayyan acewa jamhuriyar musulunci tana bukatar ganin sauran al'ummomi sun samu daukaka da 'yancinsu daga mulkin mulukiyar sauran kasashe masu danniya.



Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo na tashar talabijin din Al-alam cewa, Qazamfar Rukni Abadi jakadan kasar Iran a kasar Lebanon ya bayyan acewa jamhuriyar musulunci tana bukatar ganin sauran al'ummomi sun samu daukaka da 'yancinsu daga mulkin mulukiyar sauran kasashe masu danniya na kasashen turai.

A nasa bangaren shugaban kasar Iran Dakta Mahmoud Ahmadinejad ya ce a matsayin Iran da kuma Sudan na kasashe masu 'yanci, akwai gagarumar rawar da kasashen biyu za su iya takawa dan samar da adalci a cikin kasashen duniya.
Ahmadinejad wanda yake ganawa da sabon jakadan kasar Sudan a nan birnin Tehran Mir-qani Abubakar a wannan asabar, ya ce duk da cewa kasashen duniya masu mayaudara sun samu nasarar raba kasar Sudan gida biyu, to amma kuma har yanzu suna ci gaba da kulla wa Sudan makirci da kuma cutar da ita a fagage daban daban.
Ahmadinejad ya ce a matsayin Iran na kasar da take da kyakkyawar hulda da Sudan, to lalle kuwa kasar za ta ci gaba da yin aiki kafa da kafada da Khartum dan kare hakkokin da kuma mutuncin kasashen a matsayinsu na 'yantattu. Tun farko-farkon samun nasarar juyin juya halin Musulunci ne dai kasashen biyu suke da kyakkywar alaka a bangarori daban daban na ci gaba, kuma ko a cikin watan da ya gabata shugaba Ahmadinejad ya kai ziyarar aiki a birnin Khartum inda ya gana da shugaba Umar Hasan Albashir.
885495






captcha