IQNA

Za A Bincika Yiwuwar Bayar Da Dama A Yi Amfani Da Musulunci A Kamfe A Masar

16:33 - October 24, 2011
Lambar Labari: 2210955
Bangaren kasa da kasa, ana shirin gudanar da wani zama da zai hada dukaknin bangarorin siyasa na kasar Masar domin tattauna batun yin amfani da addinin muslunci a wajen kamfe na siyasa a kasar.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo na jaridar yaum Al-sabi cewa, bayan da kungiyar muslim Brothers ta kasar Masar ta koka kan batun hana sanya addini a cikin kamfe na siyasa, yanzu ana shirin gudanar da wani zama da zai hada dukaknin bangarorin siyasa na kasar Masar domin tattauna batun yin amfani da addinin muslunci a wajen kamfe na siyasa a kasar ta Masar baki daya.
A bangare guda kuma an gudanar za be a kasar Tunisia, adadin mutunen da suka yi zaben wakilen da za su kasance a majalisar da zata rubuta kundin tsarin milki a Tunusiya da kuma girka wanda za su yi rikon kwarya kafin babban zabe a jiya, ya kai 80% a wasu wuraren a cewar Kamel Jendubi shugaban hukumar zaben kasar ta Tunisiya a lokacin wani taron manema labarai 'yan sa'o'i kafin a rufe rumfunan zaben.

Ya ci gaba da cewa; 'yan kasar tunisiya ba su samu damar sallatar juyyin juya halin al'ummar kasar ba a ranar 14 ga watan Janeru, ranar faduwar bakin milkin Ben Ali, amma yau sun fito dafifi, sun jefa Kuria, a zaben da ya zama tamkar wata ranar sallah. Sama da mutane suka caccanci su kada kuri'unsu a wannan zabe na farko don zaben wakilan majalisa.

Wasu daga cikin masu zaben, wannan shine karo na farko da suka taba yin zabe a rayuwarsu, wakilan da aka zaba su ne zasu rubuta sabon kundin tsarin milki, da girka hukumar zartarwa ta wucin gadi da zata shirya zabubbuka a cikin shekara guda, wata tara bayan faduwar Ben Ali. Ana sa ran samun sakamakon zaben a gobe talata.
885492


captcha