IQNA

Kungiyar Nahda Ta Kasar Tunisi Ta Ti Gargadi Kan Magudin Zabe

16:32 - October 24, 2011
Lambar Labari: 2210956
Bangaren kasa da kasa, kungiyar masu kishin islama ta kasar Tunisi wato Nahda ta yi gargadi mahukunta da kuma hukumar zaben kasar da su yi hattara wajen fitar sakamakon zabe ba tare da magudi ba.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din al-alam cewa, kungiyar masu kishin islama ta kasar Tunisi wato Nahda ta yi gargadi mahukunta da kuma hukumar zaben kasar da su yi hattara wajen fitar sakamakon zabe ba tare da magudi ba kamar yadda aka saba yi a tsohuwar gwamnati.
Yanzu haka dai an bayyana cewa mutunen da suka yi zaben wakilen da za su kasance a majalisar da zata rubuta kundin tsarin milki a Tunusiya da kuma girka wanda za su yi rikon kwarya kafin babban zabe a jiya, ya kai 80% a wasu wuraren a cewar Kamel Jendubi shugaban hukumar zaben kasar ta Tunisiya a lokacin wani taron manema labarai 'yan sa'o'i kafin a rufe rumfuna.

Jami'in ya ci gaba da cewa; 'yan kasar tunisiya ba su samu damar sallatar juyyin juya halin al'ummar kasar ba a ranar 14 ga watan Janeru, ranar faduwar bakin milkin Ben Ali, amma yau sun fito dafifi, sun jefa Kuria, a zaben da ya zama tamkar wata ranar sallah. Sama da mutane million 7 suka caccanci su kada kuri'unsu a wannan zabe na farko don zaben wakilan majalisa dari biyu da saba'in da daya.

Wasu daga cikin masu zaben, wannan shine karo na farko da suka taba yin zabe a rayuwarsu, wakilan da aka zaba su ne zasu rubuta sabon kundin tsarin milki, da girka hukumar zartarwa ta wucin gadi da zata shirya zabubbuka a cikin shekara guda, wata tara bayan faduwar Ben Ali. Ana sa ran samun sakamakon zaben a gobe idan Allah ya kaimu.

885310


captcha