Bangaren siyasa da zamantakewa; Bayan da aka gina wata Otel ta kankara a arewacin Suidin da hakan ya kai ga gina wata coci ta kankara cikin nasara sai gashi a wannan karo an kaddamar da wani shiri na gina masallacin kankara a wannan kasa.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; Bayan da aka gina wata Otel ta kankara a arewacin Suidin da hakan ya kai ga gina wata coci ta kankara cikin nasara sai gashi a wannan karo an kaddamar da wani shiri na gina masallacin kankara a wannan kasa.Dan Bjork shugaban bangaren saye da sayarwa a wannan Otel din ya bayyanawa radiyon Suidin cewa: tunanin gina wannan masallaci na kankara wani kamfani ne ya bayar da shawarar yin haka domin samara da yancin addini da kuma kiyaye hakkokin kowa da kowa kamar yadda aka bawa kiristoci hakkinsu haka kuma a bawa suma musulmi hakkinsu da kiyaye masu hakkin nasu ba tare da nuna banbanci ba.
886097