IQNA

Mai Bayar Da Fatawa A kasar Lebanon ya Bukaci A Bincika Batun Imam Musa Sadr

16:46 - October 25, 2011
Lambar Labari: 2211752
Bangaren kasa da kasa, babban mai bayar da fatawa ga mabiya tafarkin iyalan gidan manzon allah a kasar Lebanon ya yi kira da a gudanar da bincike kan batun makomar Imam Musa Sadr da Mu'ammar gaddafi ya sace tare da abokan tafiyarsa biyu.


A ranar lahadin da ta gabata ne wato ashirin da uku ga watan oktoba gwamnatin Lebanon ta aike da tawaga zuwa Libya wacce ta ke kunshe da alkalai domin ganawa da mahukuntan kasar akan makomar Imam Musa Sadar. Tawagar za ta sami cikakken bayanai da su ka shafi sace malamin da ya kafa kungiyar Amal da kuma kungiyar Talakawa marasa galihu a Lebanon.

A shekarar dubu daya da dari tara da sabain da takwas ne dai Mu'ammar Gaddafi ya gayyaci Imam Musa Sadar zuwa Libya domin halartar taron shekara-shekara na cin nasarar hawansa karagar mulki da ya ke kira juyin juya hali. Sai dai tun da ya shiga cikin kasar ta Libya bai fito daga cikinta ba.

Bugu da kari gwamnatin Lebanon za ta aike da wata tawaga daga ma'aikatun harkokin waje da kuma ta shari'a zuwa Libya saboda ta gana da dukkanin wadanda sunayensu su ke da alaka da batun Imam Sadar, a gefe daya majalisar koli ta addinin musulunci a Lebanon ta dorawa gwamnatin rikon kwaryar Libya alhakin gano da bayyana makomar Imam Musa Sadar bayan gushewar shekaru 33 da shigarsa wannan kasa.

Shugaban kungiyar Amal, kuma shugaban majalisar dokoki Ustaz Nabih Barreh da ya gabatar da jawabi a taron tunawa da zagayowar shekaru 33 da bacewar Imam Musa Sadar wanda aka yi a garin Ba'alabak ya ce: Tun daga lokacin da mutanen Libya su ka fara bore ne kungiyar ta Amal tare da hadin guiwar gwamnatin Libya su ke kokari da fadi tashin ganin an gano makomar Imam Musa Sadar.

886186
captcha