IQNA

Kotun Faransa Ta Hana Gina Babban Masallaci A Marsel

Bangaren kasa da kasa; wata kotu a kasar faransa ta soke izinin gina wani masallaci mafi girma a birnin Marsel birni na biyu mafi girma a kasar ta Faransa kuma kotun ta fake ne da cewa an sabawa tsarin gina gurin ajiyar motoci a masallacin da kuma cewa bai yi daidai da tsarin garin ba.


Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: wata kotu a kasar faransa ta soke izinin gina wani masallaci mafi girma a birnin Marsel birni na biyu mafi girma a kasar ta Faransa kuma kotun ta fake ne da cewa an sabawa tsarin gina gurin ajiyar motoci a masallacin da kuma cewa bai yi daidai da tsarin garin ba.Wannan ana ganinsa a wani mataki da salo irin na adawa da kula makirci kan musulmi da addinin musulunci da kuma nuna kama kan musulmi da musulunci a kasashen yammacin Turai irin su faransa domin ko ba komi izinin gina wannan masallaci a birnin na Masrsel tun shekara ta dubu biyu da tara miladiya ne aka bada kuma sabo da adawar da mazauna yanki da makircin turawan yankin aka dakatar da gina shi kuma yan siyasa da kungiyoyi masu wuce gonad a iri a faransa sun nuna adawa saboda girma da fadin masallacin.

888900